1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: An sami karuwar 'yan gudun hijira

Abdullahi Tanko Bala
June 18, 2021

Wani rahoto da hukumar kula da 'yan guduin hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar yace an sami karuwar mutane da ke yin hijira saboda yake-yake da tashe-tashen a bara duk da annobar corona da aka yi fama da ita.

https://p.dw.com/p/3vBJL
Griechenland Flüchtlingslager Samos
Hoto: Panagiotis Balaskas/AP/picture alliance

Rahoton yace zuwa karshen shekarar 2020 mutane fiye da miliyan 82 aka tilastawa yin kaura daga muhallansu adadin da ya rubanya yawan wadanda suka yi hijira shekaru goma da suka wuce.

Kakakin hukumar kula da yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya Chris Melzer ya shaida wa tashar DW cewa kashi 86 cikin dari na 'yan gudun hijirar suna kasashe ne masu tasowa wadanda kuma ke fama da matsalolin karancin abinci da dai sauransu.

Fiye da kashi biyu cikin kashi na uku na wadanda aka amince da su a hukumance a matsayin 'yan gudun hijira sun fito ne daga kasashe biyar da suka hada da Syria da Venezuela da Afghanistan da Sudan ta Kudu da kuma Myanmar a cewar rahoton.

Kwamishinan kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Fillipo Grandi yace a Afrika tashe-tashen hankula da matsalolin sauyin yanayi sun haifar da kwararar 'yan gudun hijira a kasashen Mozambique da Habasha da yankin Tigray yayin da aka sami dubban 'yan gudun hijira na cikin gida a yankin Afirka kudu da hamadar sahara.