MDD: Wasu mutum miliyan 1 za su tserewa Sudan
June 28, 2023Talla
Kawo yanzu dai kimanin mutane 600,000 ne suka tsere wa kasar zuwa kasashen Masar da Chadi da Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Mataimakin kwamishnan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, Raouf Mazou ya ce sun yi kiyasin ne saboda yadda abubuwa ke tafiya a Sudan, yayin da rikici tsakanin shugaban dakarun sojin kasar Abdel-Fattah Burhan da kuma shugaban mayakan RSF Mohammed Hamdan Dagalo ke shiga mako na 10.
Ko da yake bangarorin biyu da ba sa ga maciji da juna sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta albarkacin bukukuwan babbar salla da al'umma musulman duniya ke gudanarwa.