1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta nemi Saudiyya ta janye takunkumi a Yemen

Yusuf Bala Nayaya
November 7, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a janye kulle iyakar da ke zama tarnaki ga kai kayan agaji ga dubban al'umma a kasar Yemen bayan rufe filin jiragen sama da tashar jirgin ruwa da iyaka ta kasa.

https://p.dw.com/p/2nBZ5
Saudi Arabien Jizan Grenze Jemen
Hoto: Getty Images/AFP/F. Nureldine

A cewar Jens Laerke da ke magana da yawun hukumar agajin gaggawa ta OCHA a Majalisar Dinkin Duniya, kimanin kashi 80 zuwa 90 cikin dari na kayan agaji da suke bayarwa na zuwa ne ta hanyoyin iyakar kasa da tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama a kasar ta Yemen.

Kasar Yemen dai na zama daya daga cikin wurare mafiya muni da ake fama da matsala ta rashin abinci a duniya inda kimanin mutane miliyan bakwai ke fama da matsala ta rashin wadataccen abinci kuma ke dogaro da abincin agaji. Rufe iyakokin dai tuni ya fara shafar al'umma inda farashin man fetir ya daga da kashi 60 cikin dari haka ma gas na girki farashinsa ya ninka.