1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gidauniyar tallafa wa Turkiyya bayan girgizar kasa

February 16, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta kafa gidauniya domin tattara kudade da zummar tallafa wa kasar Turkiyya bayan mummunar girgizar kasar da ta fuskanta

https://p.dw.com/p/4Nc9T
Erdbeben Türkei Gaziantep
Hoto: SUHAIB SALEM/REUTERS

Kaddamar da gidauniyar na zuwa ne a daidai lokacin da aka kiyasta cewa yawan wadanda suka mutu sun kai akalla mutane dubu arba'in a kasar da Turkiyya da kuma makobciyarta Siriya.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ya sanar da cewa ana bukatar dala biliyan daya domin kai dauki ga mutane miliyan biyar da dubu dari biyu a tsawon watanni uku inda kuma ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka don tattara wadannan kudaden da ake bukata cikin gaggawa domin fuskantar abin da ya kira iftila'in mafi girma na wannan lokaci.

Guteress ya kuma kara da cewa lokaci ya yi da kasashen duniya za su tallafa wa Turkiyya ba tare da bata lokaci ba kamar yadda a baya ita ma kasar ta ke taimaka wa kasashe da ke cikin halin  bukata makamancin wannan.