1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta dakatar da Rasha

April 8, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da kasar Rasha daga hukumarta na kare hakkin bil'Adama saboda mamayar da ta yi wa kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/49eBL
Ukraine-Krieg - UN-Menschenrechtsrat
Hoto: John Minchillo/AP/dpa/picture alliance

Matakin katse huldar diflomasiyyar na zuwa ne bayan da kasashe 7 masu karfin masana'antu da kungiyar Tarayyar Turai da kuma Washington suka kara kakaba wa Rashar takunkumai na karya tattalin arziki bayan fitowar wasu hotuna da ke nuna irin ta'assar da Rashar ta yi a garuruwan Bucha da Mariupol na kasar Ukraine.

Ana martanin, gwamnatin Moscow ta yi watsi da kuru'ar dakatar wa da aka kada a zauren Majalisar Dinkin Duniya, ta na baiyana hakan a matsayin abun da ya sabawa ka'ida a siyasance. Yayin da ake ci gaba da zargin Rashar da kaddamar da hare-hare kan fararen hula a Ukraine, hukumomin na cewa sun gano wasu gawawwaki cikin baraguzan gini a yankin Borodianka da ke kusa da Kyiv babban birnin Ukraine.

Shugaba Volodmyr Zelensky dai ya nuna fargabarsa kan yiwuwar barnar da Rasha ta yi a Borodianka din ya fi na Bucha muni, yankunan da kasashen yamma na Turai ke zargin dakarun Rasha da aikata laifukan yaki.