1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MDD ta ce yakin Sudan ya jefa mutane miliyan 18 cikin yunwa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 14, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yunwar ta fi tsanani a Khartoum babban birnin kasar da ke da tarin jama'a, sai yankin Darfur da kuma Kordofan da suka jima cikin rikici

https://p.dw.com/p/4a9SJ
Hoto: AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin Sudan ya jefa mutane miliyan 18 cikin halin tsananin yunwa da ke bukatar agajin gaggawa, daga cikin 'yan kasar miliyan 30 da ke cikin mawuyacin yanayi a halin yanzu.

Karin bayani:Jagororin bangarori biyu da ke rikici da juna a Sudan sun amince da ganawa don tsagaita wuta

Hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yunwar ta fi tsanani a Khartoum babban birnin kasar da ke da tarin jama'a, sai yankin Darfur da kuma Kordofan da suka jima suna fuskantar tashe-tashen hankula shekara da shekaru.

Karin bayani:Al-Burhan ya bukaci MDD ta kawo karshen ayyukanta a Sudan

Tun a cikin watan Afrilun da ya gabata ne dai rikici ya barke tsakanin dakarun sojin kasar da ke karkashin ikon Janar Abdel Fattah al-Burhan da na RSF da ke karshin jagorancin Mohamed Hamdan Dagalo, wanda ya hallaka mutane sama da dubu goma sha biyu.