Brazil :MDD ta ce a bar Lula ya tsaya takara
August 17, 2018A cikin wata takaitacciyar sanarwa da ya fitar kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya kamata mahukuntan a kasar Brazil su bai wa tsohon shugaban damar gudanar da yakin neman zabe ko da daga gidan kason da yake tsare ne, matukar dai kotu ba ta kare sauraran kararrakin da ya shigar a gabanta ba.
A ranar 27 ga watan Yulin da ya gabata ne dai lauyoyin Mista Lula mai shekaru 72 a duniya suka shigar da koke a gaban kwamitin na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya kunshi kwararru a fannin ilimin shari'a domin ya bayyana matsayinsa kan makomar takarar tsohon shugaban na Brazil da ake tsare da shi a bisa laifin cin hanci.
Tuni a ranar Larabar da ta gabata dai jam'iyarsa ta PT ta tsayar da takarar tasa, sai dai akwai yiwuwar kotu ta yi watsi da ita kasancewar dokokin kasar sun haramta tsayawa takara ga duk mutumin da kotun daukaka kara ta yanke wa hukuncin kaso bayan samunshi da laifi.