1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya za ta tallafawa Najeriya

Uwais Abubakar Idris RGB
June 15, 2020

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shirin nemawa Najeriya tallafi na dala milIyan 182 don bunkasa tattalin arzikin kasar da annobar Coronavirus ta yi wa nakassu amma ta ce miliyoyi ka iya rasa aikin yi.

https://p.dw.com/p/3dmU4
UN-Generalversammlung in New York | Muhammadu Buhari, Präsident Nigeria
Hoto: Reuters/L. Jackson

Majalisar Dinkin Duniya ta baiyana shirin nemawa Najeriya tallafi na dala milIyan 182 don bunkasa tattalin arzikin kasar saboda matsalar da annobar Coronavirus ta haifar, sai dai ta ce miliyoyi a kasar za su rasa aikin yi a dalilin wannan matsala. Wannan yunkuri da Majalisar Dinkin Duniyar ke yi dai  labari ne mai dadin ji ga Najeriyar da annobar ta Covid-19  ke ci gaba da yi wa illa ga harkokin tattalin arziki da ma zamantakewar al’ummarta, inda tuni gwamnatin ta kai ga bara da cewa tattalin arziki na fuskantar sake shiga wata sabuwar masassara ta koma baya. 

A sanarwar da majalisar a karkashin shirinta na samar da abinci ta fitar a Abuja, ta bayyana muhimmancin yin hakan. Kakakin shirin abincin na Majalisar Dinkin Duniyar Elisabeth Byrs ta  tabo batun halin da yara da ke cikin mawuyacin hali saboda matsalar rashin wadataccen abinci musamman mai gina jiki da nufin taimaka masu a jihohin Lagos da Abuja da kuma Kaduna.  Yayin da yara  da mata milyan bakwai da dubu dari tara a yankin arewa Maso Gabas da ke hali na matukar bukatar taimakao saboda barazana ta rashin abinci.

Tuni dai Kungiyar Kwadagon Najeriyar ta bayyana  tuntubar gwamnati a kan batun korari ma’aikata saboda koma bayan tattalin arziki da cutar ta Covid-19, domin duk da alkawarin da gwamnatin ta yi a kan ba wanda za’a kora daga aiki,  wasu kamfanoni na ci gaba da fatattakar ma’aikatan.  Za’a sa ido a ga tasirin da wannan yunkuri na Majalisar Dinkin Duniyar zai iya yi a kokari na tallafawa tattalin arzikin Najeriyar.