MDD: Saudiyya ta keta dokokin yaki a Yemen
October 4, 2017Saudiyya da ke taimaka wa gwamnatin Shugaba Abdourabuh Mansour Hadi don yakar 'yan tawayen Houthi ta sami kanta a cikin layin kasashen da suka taka dokokin yaki na duniya bisa rawar da kasar ta taka a rikicin kasar Yemen da ya lakume rayukan mutane fiye da dubu biyu a bara. Akalla 700 daga ciki wadannan alkaluman yara kanana ne inji rahoton Majalisar Dinkin Duniya, abin da ke nufin kashi 50 cikin 100 na yaran da suka hallaka a yakin Yemen a bara ya auku ne a sanadiyyar hare haren da dakarun kawance da Saudiyya ke jagoranta suka kaddamar a cikin kasar.
A daya bangaren kuwa Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana kasar ta Yemen a matsayin kasar da ke cikin mawuyacin hali da tsananin bukatar taimako ganin mutane akalla miliyan bakwai ne ke fuskantar barazanar yunwa da kuma barkewar cutar amai da gudawa yanzu haka a kasar ta Yemen.