1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Rikici na rutsawa da miliyoyin mutane

January 26, 2022

Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa fiye da mutane miliyan biyar ne rikici ya rutsa da su a kasashen Afghanistan da Libya da Yemen da kuma Siriya.

https://p.dw.com/p/4659W
COP26 in Glasgow
Hoto: Yves Herman/Pool/REUTERS

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce a lokuta da dama an yi ta kai wa fararen hula hari da zumar kadammar da hare-hare kan masu tada kayar baya wanda hakan ke rutsawa da wadanda ba su ji ba su gani ba.

Gutarres ya ce hakan na tilasta wa fararen hula killace kansu a gidaje wanda kuma ke jefa miliyoyin jama'a cikin kangin yunwa.

Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma bukaci sojoji su mutunta dokokin kasa da kasa na kaucewa kai hari kan fararen hula da gine-ginen gwamnati da kuma gujewa amfani da ababen fashewa a cikin bainar jama'a.