1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zargin Koriya ta Arewa da sabunta nukiliya

Abdul-raheem Hassan
February 9, 2021

Jami'an da ke lura da takunkumin da aka sawa Koriya ta Arewa sun ce gwamnatin Kim Jong Un, ta tanadi kayan sarrafa makaman nukiliya, kuma ta shirya sake gwajin sabbin makaman kare dangi da ta sake fasalta su.

https://p.dw.com/p/3p5iJ
Nordkorea | Feierlichkeiten 75 Jahre Arbeiterpartei WPK
Hoto: Reuters/KCNA

Kwararru a harkar makamashi da makaman kare dangi a Majalisar Dinkin Duniya, suna zargin Koriya ta Arewa na cigaba da sarrafa sabbin nau'un makamai masu linzami, tare da neman kayan sarrafa makaman da kimiyyarsu daga saura kasashen duniya.

A 2016 kwamitin sulhu na MDD ta kakabawa Koriya ta Arewa tsauraran takunkumin bayan gwajin makamanta na nukiliyar na farko, inda aka haramta mata fitar da kaya tare da takaita shigo da wasu kayayyakin daga kasashen waje da zimmar tilasta ta rusa tashoshin nukiliyarta.