Majalisar Dinkin Duniya ta yi na'am da shelar 'yan Huthis
September 22, 2019Talla
A cikin wata sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa ta bukaci 'yan tawayen Houthis da su tabbatar da wata yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Disamba, musamman batun musanyar fursunonin yaki, tana mai cewa hanyar siyasa ce kawai za ta iya kawo karshen yakin da ya daidaita kasar ta Yemen.
Sai dai da take mayar da martani game da marakin kungiyar ta 'yan tawayen Houthis, kasar Saudiyya ta ce ba za ta iya tabbatar matakin ba kawai a baki face sai ta gani a zahiri.