1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar yara na cikin hadari

Abdullahi Tanko Bala
February 19, 2020

Kananan yara kimanin miliyan 250 a fadin duniya na fuskantar hadarin sauyin yanayi na matsalolin rayuwa da suka hada da rashin abinci mai gina jiki da kuma talauci a cewar wani sabon rahoto na Majalisar Dinkin Duniya

https://p.dw.com/p/3Xz2X
Symbolbild | Klimawandel | Dürre | Honduras
Hoto: AFP/Getty Images/O. Sierra

Makomar kananan yara a duniya na cikin hadari yayin da kasashe a fadin duniya suka kasa shawo kan sauyin yanayi da samar da ingantaccen tsaftar muhalli da koshin lafiya a cewar wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar.

Rahoton wanda kwararru fiye da 40 kan rayuwar yara da lafiyarsu suka rubuta ya yi nazari kan sauyin yanayi da lalacewar kasa da kaurar jama'a da rigingimu da kuma rashin daidaito na samun abun hannu a tsakanin al'umma da kuma makomar yara a nan gaba.

Rahoton na hadin kungiya tsakanin hukumar lafiya ta duniya WHO da asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF yace yayin da yara a kasashe masu arziki suke da damar samun rayuwa mai inganci, a waje guda wadannan kasashe sune kuma suke fitar da hayakin masana'antu da gurbata yanayi da kassara rayuwa da makomar yara.