1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin Khalifa Haftar da dauko sojan haya daga waje

Abdoulaye Mamane Amadou
May 7, 2020

Wani rahoton bincike na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa ana amfani da sojojin haya 'yan asalin kasar Rasha a yakin basasar kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/3bu84
Libyen Khalifa Haftar
Hoto: AFP/A. Doma

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya da kawo yanzu ba a kai ga wallafa shi ba, ya yi nuni da cewa madugun yakin Libiya Khalifa Haftar na amfani da sojojin hayar ne a fafutikar da yake na karbe iko daga hannun gwamnatin Tripoli mai goyon bayan Majalisar.

Ko da yake kwararrun na MDD ba su kai ga tantance adadin sojan hayar da Khalifa Haftar ke amfani da su ba, to amma sai dai ana zargin ko sun haura daga 800 zuwa 1,200, kana kuma ana danganta su da shugaban kasar Rasha Vladimir Poutine.