SiyasaAfirka
MDD: Kasashe bakwai sun gaza biya kudinsu
January 18, 2021Talla
Kasashen bakwai da suka hada da Iran sun rasa damar kada kuri'a a babbban zauren Majalisar Dinkin Duniya saboda rashin biyan da aka saba, kamar yadda Antonio Guterres babban sakataren majalisar ya bayyana a wannan Litinin.
Wani kudiri na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci dakatar da kuri'ar da kasa za ta iya kadawa muddun ta gaza biyan kudin da aka tsara ake bai wa majalisar tsakanin kasashen duniya inda rashin biyan ya wuce shekara biyu.
Sauran kasashe shida su ne: Jamhuriyar Nijar, Libiya, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Kwango Brazzaville, Sudan ta Kudu da Zimbabuwe kamar yadda babban sakataren ya rubuta ga shugaba babban zauren majalisar Volkan Bozkir dan kasar Turkiyya.