1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Jama'a na fama da yunwa a Tigray

Abdullahi Tanko Bala
June 11, 2021

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum 350,000 na fuskantar matsananciyar yunwa wasu miliyoyi kuma na cikin hadari a yankin Tigray na kasar Habasha.

https://p.dw.com/p/3ulOu
Äthiopien Tigray-Krise
Hoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Kungiyoyin agaji sun dora alhakin halin da aka shiga na yunwa a yankin Tigray akan rikicin baya bayan nan da ya barke a yankin.

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya yace sama da mutum miliyan biyar na bukatar tallafin abinci.

Kungiyoyin agaji sun ce halin da ake ciki a yankin na Tigray shi ne mafi muni da aka gani tun bayan annobar fari da ta auku a Somalia a shekarun 2010 zuwa 2012 da ta hallaka yan Somalia fiye da dubu 250 yawancin su kananan yara.

Wani babban jami'in kungiyar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya Luca Russo yace yunwar ta yi tsanani kuma mutane na mutuwa musamman yara kanana wadanda basa samun abin da za su ci.