1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsalandn daga ketare a Libiya

Binta Aliyu Zurmi
July 9, 2020

Babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi game da masu tsoma baki daga kasashen ketare a rikicin kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/3f0ay
Antonio Guterres bei einer Pressekonferenz in Äthiopien
Hoto: AFP via Getty Images

Babban sakataren ya kara da cewar a halin da ake ciki yanzu, wakilan majalisar na can a kasar ta Libiya suna kokarin ganin an cimma tsagaita wuta tsakanin dakarun da ke fada domin cetar da rayukan alumma. 

Guterres ya ce daga farkon watan Afirilu zuwa karshen watan Yuni an kashe sama da fararen huda dari tare da jikkata sama da dari biyu da hamsin, wanda sakataren ya ce na zama sama da kaso 170 idan aka kwatanta da kwatan farko na wannan shekarar.