1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akwai yuwuwar barkewar yunwa a Somaliya a shekara ta 2016

Kamaluddeen SaniJanuary 19, 2016

Majalisar dinkin duniya ta ce akwai yuwuwar samun yunwa a kasar Somaliya a wannan shekarar da muke ciki sakamakon ambaliyar ruwa da fari gami da dubban 'yan kasashen Yemen da Kenya da ke shiga kasar.

https://p.dw.com/p/1HgDS
Karte Somaliland Somalia Englisch
Hoto: DW

Hukumar ta ce daya daga cikin mutane biyu na bukatar taimako a Somaliya a yayin da sama da dubu dari 300 da dukkanin su kana nan yara ne kuma 'yan kasa da shekaru biyar na fusakantar rashin abinci mai sanya kuzari.

Kazalika karin dubu 56 daga cikin su na iya mutuwa muddin dai ba a basu kulawar data kama cesu ba.

'Yan Somaliya dai kimanin sama da miliyan daya ne suka bar muhallan su a yayin da sama da karin miliyan ke samun mafaka a kasashen dake makwafta ka da ita sakamakon rikice-rikice dake addabar kasar.