Mazauna Agadez na fama da tsadar kudin haya
July 25, 2017Samun gidajen haya masu arha na zama kalubale a Agadez bisa la'akari da yawan al'umma, ko da ya ke birnin na kan gaba wajen karbar baki daga kasashe makota, lamarin da ya sa rabin al'umma da ke rayuwa a birnin ke fama da matsalar karancin muhalli.
Har yanzu wasu mazauna birnin na agadez na ganin cewa akwai isassun gidaje na haya da mutane za su iya zaba, amma ba su da kudin da za su iya biya. Babbar matsalar ita ce akasarin masu gidajen haya na so a biya kudin hayar na wasu watanni a dunkule kamin a shiga gidajen.
Hanya daya da za a bi domin cike gibin da ake da shi wajen karancin gidajen haya shi ne samar da gidaje masu inganci da saukin kudi, wanan kuma sai ma'aikatar magajin gari ta tallafawa masu karamin karfi wajen samar musu filayen gini na kan su cikin rahuwa saboda a cewar wasu mazauna garin Agadez, sau tari a duk lokacin da ma'aikatar ke sayar da filaye masu hali ne ke anfana da garabasar ba talakawa ba.