1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar masu girki ta duniya

October 20, 2020

A yayin da ake bikin ranar 20 ga watan Oktoba da MajalisarDinkin Duniya ta kebe a matsayin ranar masu girki ta Duniya, a Jamhuriyar Nijar mazan da ke yin girki a otel-otel sun ce sun fi mata iya girki.

https://p.dw.com/p/3kBrC
DW Euromaxx - 50k - Afrika6
Kwararren mai dafa abinci a gidan abinci na Pan Afrika da ke Berlin fadar gwamnatin JamusHoto: Lena Ganssmann

Ita dai ranar girkin ta duniya ta samo asali ne daga shekara ta 2004, yayin da aka tabbatar da kwarewar shugabanin iya dafuwa a duniya. To sai dai a bana an fuskanci tarin kalubale na matsalolin da annobar coronavirus ta haifar, wadanda suka shafi fannoni da dama ciki har da shashen dafe-dafen abinci a gidajen sayar da abinci wato restaurant.

Muhawara dai ta barke tsakanin masu yin girkin maza da kuma wadanda ke kiran kansu 'yan gado wato mata a wani gidan sayar da abinci a Jamhuriyar Nijar. A irin wannan rana dai, masu yin girkin na kokarin nuna bajinta da kuma iya girki, kama daga masu yin abincin gargajiya zuwa na zamani na ci gaba da wasa kawunasu.