1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin mayar da Mali hannun farar hula

Ramatu Garba Baba
October 21, 2021

Wata tawagar Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na shirin ziyarar Mali a kokarin ganin sojojin da suka kwace mulki sun mika madafun iko hannun gwamnatin farar hula.

https://p.dw.com/p/41yoy
USA | UN-Sicherheitsrat zu Äthiopien
Hoto: Loey Felipe/UN Photo/Xinhua/picture alliance

Wakilan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniyan na shirin ziyarar Mali don ganin an mayar da shugabancin kasar a hannun gwamnatin farar hula, a karshen wannnan makon tawagar, za ta isa kasar  inda za su tattauna da gwamnatin na yanzu a kokarin shawo kan sojojin da suka kwace mulki don ganin sun mayar da kasar kan tafarkin demokradiyya.

Daya daga cikin wakilan, Abdou Abarry, Jakadan Jamhuriyyar Nijar a Majalisar Dinkin Duniya, ya ce, yankin Sahel na fuskantar matsanancin rashin zaman lafiya ga halin da miliyoyi ke ciki na bukatar taimako a sakamakon aiyukan mayakan jihadi da suka yi kaka gida a yankin Sahel, saboda haka akwai bukatar daukar matakin daidaita kasar kafin samun galaba kan masu tayar da kayar baya.

Kwamitin na fatan ganin sojojin sun bayar da hadin kai, a tsayar da ranar da kasar za ta gudanar da zaben shugaban kasar. Kafin halin da kasar ta tsinci kai a yanzu, Mali da ta fuskanci juyin mulki har sau biyu a cikin watannin tara, dubbai suka rasa rayukansu wasu daruruwa suka rasa matsuguni a sakamakon tashe-tashen hankula daga aiyukan masu tayar da kayar baya.