1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Jamus: Mayar da kayan tarihin Afirka

March 29, 2022

Yawancin gidajen tarihi na Jamus sun jera kayan tarihi na 'yan Afirka abubuwan da aka wawushe a lokacin mulkin mallaka cikin kayan tarihinsu, a daidai lokacin da muhawarar mayarwa da Afirka kayan ke kara zafi.

https://p.dw.com/p/49Bi6
Gidana kayan tarihi na Leipziger Grassi-Museum
Kayan tarihin AfirkaHoto: picture-alliance/dpa/P.Endig

Kayan tarihin Afirkan da a yanzu haka ke cikin na Jamus dai, sun hadar da kayayyakin fasaha da na ibada, musamman na addini. Tsawon shekaru da dama cibiyoyin al'adun Jamus suka fara tattaunawa kan hanyoyin ci gaba da mayar da kayayyakin ga 'yan Afirka, tare da hadin gwiwar kasashen da aka yi wa satar. Yanzu haka kusan gidaje 20 na al'adu a Jamus, suna da dubban abubuwa da aka samu a lokacin mulkin mallaka. A Jamus dai an dukufa kan tunanin tsarin mayar da wannan kayan tarihi  na gargajiya na al'adu ga mamallakansu na asali, bayan wani rahoto da wata cibiya ta Faransa ta Sarr Savoy ta mika ga hukumomin kasar a shekara ta 2018 kan bukatar kasashen da aka yi wa wasoson kayan tarihin da Jamus din ta yi wa mulkin mallaka na wani dan lokaci

Wannan rahoto ya sa sauran kasashen Turai, nuna shakku kan yadda aka samar da tarin kayan tarihinsu. Sake tattara kayayyakin domin mayar da su, aiki ne mai wuya. Da farko sai an tantance yanayin da aka samu kayayyakin kafin kuma a kididdigesu. Akwai dai kayayyakin tarihin da Jamus ta kwaso daga Afirka, wadanda kawo yanzu addadinsu ya kai dubu 70 da ake kokarin samar da hanyar internet da za ta hada kayan al'adun mulkin mallakar daga dukkan gidajen tarihi na Jamus. Hukumomin na Jamus sun bude hanya ga kwarraru daga kassahen waje kan sha'anin al'adu ga masu sha'awa, domin zuwa yin aiki a Jamus din na tsawon lokaci a kan kayayyakin tarihin Afirkan da aka sato domin aikin tantancesu.