Afirka ta Kudu ce karama tsakanin kasashen BRICS
July 8, 2015A ranakun takwas da tara ga watan nan na Yuli, kungiyar kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa wato BRICS ke gudanar da taronta karo na bakwai a kasar Rasha daya daga cikin kasashe mambobin kungiyar. Kasashen na kungiyar BRICS dai sun hadar da Barazil da Rasha da Indiya da kuma Afirka ta Kudu. Sai dai baki dayan kasashen ba wai yawan al'umma kawai suka fi Afirka ta Kudu ba har ma da karfin tattalin arziki. Misali tattalin arzikin kasar China ya ninka na Afirka ta Kudu har sau 28.
Shigar Afirka ta Kudun dai cikin wannan kungiya ta BRICS a shekara ta 2010 ya samu karbuwa daga kasashen duniya baki daya ta la'akari da yadda tattalin arzikin kasar ke bunkasa da kimanin kaso biyar zuwa 10 idan aka kwatanta da na kasashen kungiyar EU da ke bunkasa da kaso biyu kacal a wancan lokaci.
Karfin tattalin Afirka ta Kudu ya ragu
A wancan lokacin dai China na yi wa kasar Afirka ta Kudu kallon mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka. Kamar yadda Razia Khan kwararriyar masaniyar tattalin arziki a bankin London Standard Chartered Bank, ke cewa a hirar da ta yi da tashar DW:
"A baya Afirka ta Kudu ba wai kawai ta kasance mafi ci-gaba ba ne a fannin raya kasa kawai har ma a fannin tattalin arziki a Afirka baki daya. Sai dai bayan da Najeriya ta sanar da irin bunksar tattalin arzikin da take da shi a shekarar da ta gabata, abin tambaya shi ne wacce kasa ce ta fi karfin tattalin arziki a Afirka?"
Kasar China dai ta zuba makudan kudade da yawansu ya kai akalla dalar Amirka biliyan 15 a nahiyar Afirka a bangaren sufuri da gine-gine kana tana shigar da kaya masu rahusa a kasuwannin Afirka. A hannu guda ita ma kasar Afirka ta Kudu ta ji dadi gaya kuma tana alfahari da shigarta cikin kungiyar ta BRICS ta kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da ke kokarin yin gogayya da kungiyoyin kasashe irinsu G7 da kuma G20.
Isassun kayayyakin more rayuwa
Afirka ta Kudu dai na da arzikin albarkatun kasa da suka hadar da zinare da gawayi da lu'u-lu'u da ma ma'adinin Platinum. Ba kamar Najeriya ba, Afirka ta Kudu tana da wadatattun kayayyakin more rayuwa da kuma yanayin bunkasar kasuwanci mai kyau. A cewar Srijit Mishra, wani masanin tattalin arziki a cibiyar bunkasa bincike ta Indira Ghandi da ke Indiya, kasar da ke zaman mamba a kungiyar ta BRICS wadda kuma ke bukatar irin wadannan ma'adinai da Afirka ta Kudun ke da su.
"Afirka ta Kudu da Indiya suna da dangantaka ta tarihi a tsakaninsu. Mahatma Ghandi ya fara bincikensa na magance tashe-tashen hankula ne a kasar Afirka ta Kudu."
A cewar Razia Khan duk da yake karfin tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu bai kai na China da Indiya muhimmanci ba, amma yana da matukar amfani a samu kasar Afirka a cikin kungiyar ta BRICS. Ta kara da cewa Afirka ta Kudun na cin gajiyar zamowa mamba a kungiyar a duniya baki daya tana mai cewa:
"Ko da yake tattalin arzikin kasar ta Afirka ta Kudu ya dan ja baya a 'yan shekarun nan, wannan ba shi ne abu mafi muhimmanci ba, muhimmin abu shi ne wacce irin gajiyar da kasashen kungiyar ke ci a siyasance. Dukkan kasashen kungiyar ta BRICS na cin gajiyar kasancewar Afirka ta Kudu cikin kungiyar musamman ma China."
Kungiyar ta BRICS din dai na son ta yi gogayya ne da tattalin arzikin kasashen nahiyar Turai da bunkasarsa ta samo asali tun bayan yakin duniya na biyu. A dangane da haka ne kungiyar ta kudiri aniyar kafa bankin New Development Bank da zummar bunkasa tattalin arzikinta wanda suka fara da zuba kudi kimanin dalar Amirka biliyan 50 kafin daga bisani su kara zuwa biliyan 100. A cewar shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma a tsawon shekara guda da bankin ya yi, an samu kyakkyawan ci gaba da zai kawo sauyi a fannin tattalin arzikin duniya baki daya.