1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsanancin fada a gabashin Ukraine

September 29, 2014

Mutane da dama sun hallaka sakamakon gagarumin artabu da ake yi tsakanin 'yan awaren gabashin Ukraine da ke goyon bayan Rasha da kuma dakarun gwamnati.

https://p.dw.com/p/1DMdy
Hoto: picture-alliance/dpa

Rahotanni sun nunar da cewa wannan shi ne fada mafi muni da aka shafe tsahon mako guda ana gwabzawa tsakanin bangarorin biyu, inda fiye da mutane 10 suka rasa rayukansu yayin da wasu 32 suka jikata.

Dakarun gwamnatin Kiev sun sanar da cewa sojoji tara ne suka sheka barzahu yayin da wasu 27 suka jikkata. Ita ma a nata bangaren majalisar gudanarwar yankin Donetsk ta sanar da mutuwar fararen hula uku inda wasu biyar kuma suka jikkata a fafatawar. Wanna dai na faruwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma tsakaninsu a ranar biyar ga wannan wata na Satumba da muke ciki.

A ranar 20 ga wannan watan dai wakilan Rasha da Ukraine da kuma 'yan awaren sun kara cimma wata sabuwar yarjejeniya da ta bukaci kowanne bangare ya janye tankokin yakinsa daga inda suka ja daga, domin ba da dama ga shirin tsagaita wutar ya gudana yadda ya kamata.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo