1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar yinwa tana addabar al'ummar Yemen

September 23, 2011

A yayin da ake ci gaba da yin fito-na-fito a tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da masu adawa da ita, ƙungiyoyin agaji sun koka game da yawan jama'ar dake mutuwa sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar

https://p.dw.com/p/12fXI
Shugaba Ali Abdullah Saleh na YemenHoto: picture-alliance/ dpa

Tun bayan ɓarkewar boren neman kawar da mulkin shugaba Ali Abdallah Saleh na ƙasar Yemen cikin watan Janairu ne dai, wasu daga cikin al'ummomin ƙasar suka shiga cikin matsanancin rayuwa, sakamakon ci gaba da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da kuma tsadar kayayyakin rayuwa ta yau da kullum, musamman tashin farashin man fetur daya riɓanya na da har sau 500. A cewar ƙungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa ta Oxfam, a yanzun nan da ake batu dai aƙalla kowanne mutum guda cikin Yemenawa ukku ne ke fuskantar matsalar nyunwa a kowace rana saboda rikicin siyasar. Richard Standforth, jami'in dake kula da harkokin Yemen a ƙungiyar agaji ta Oxfam ya ce abin taƙaici ne ganin cewar a kullum 'yan ƙasar da yawan su yakai miliyan 22 suna ƙara shiga cikin matsalolin rayuwa ne:

" Idan muka taɓo batun ruwan sha kaɗai, a kwanakin baya bayannan dana je Yemen Iyalai da dama ne suka shaida mini cewar farashin da suke biya a yanzu ya riɓanya na da har sau bakwai. Jama'a na fusksatar matsala wajen samun Gas domin girki. Gashi mutane ba sa samun damar yin aiki saboda tashin hankalin, wanda ma ya janyo tsadar farashin man fetur. A lokacinn dana ziyarci ƙasar ana ɗauke wutar lantarki na sa'oi da dama, kuma idan babu wutar mutane ba za su iya kunna injinun da za su ba su ruwan sha ba, kana ba za su sami damar jigilar kayayyakin abinci zuwa ga sassan ƙasar ba. Saboda haka yanayin ya jefa su cikin mawuyacin hali."

Wasu sojin Yemen sun bi sahun masu adawa da gwamnati

Jemen Demonstration gegen Regierung Flagge in Sanaa
Boren neman kifar da gwamnatin shugaba SalehHoto: picture alliance / dpa

Ko da shike jerin zanga-zangar neman kawar da mulkin shugaba Saleh na kimanin shekaru 30 sun faro ne a tsakanin fararen hula, amma daga baya sun yaɗu hatta a cikin sojojin ƙasar waɗanda wasu daga cikin su ma suka bi sahun masu boren wajen bijirewa gwamnati, abinda kuma a cewar Anette Büchs ƙwararriya akan sha'anin Yemen dake cibiyar Giga a birnin Hamburg anan Jamus hakan ya dagula matsalar:

" A tunani, wannan arangama ce a tsakanin magoya bayan shugaba Saleh da kuma masu adawa da shi. Da farko a tsakanin fararen hula ne, daga baya ta yaɗu cikin rundunar sojin ƙasar, amma a yanzu magoya bayan Saleh sun fi ƙarfi."

OXFAM Logo
Tambarin ƙungiyar agajin OxfamHoto: AP Graphics

Ƙungiyoyin agaji sun yi kira ga tallafawa al'ummar Yemen

Tuni dai hukumomin agaji suka yi gargaɗin fuskantar babbar matsala ga rayuwar al'umma a ƙasar Yemen, muddin dai al'ummomin ƙasa da ƙasa basu yi namijin ƙoƙari ba wajen shawo kan matsanancin rayuwar da suke ciki. A cewar Richard Stanforth ƙungiyar agajin Oxfam halin ko oho ne duniya ke nunawa ƙasar:

" A Libiya munga an samar da fiye da kuɗi dalar Amirka miliyan dubu ɗaya ga ƙasar tunma a lokacin da ake tsananin yaƙin ana tallafawa bil'adama daga ƙasashen Larabawa da ma na yammacin duniya, kuma ba a yin kwatakwacin hakan a Yemen. Masar ta sami rancen kuɗi dalar Amirka miliyan dubu huɗu da 500 daga babban bankin duniya, kana Tunisia ta sami rancen kuɗi na fiye da dalar Amirka miliyan dubu ɗaya daga bankin. Sai dai babu wata huɓɓasar da masu bada agaji suke yi a Yemen."

A cewar ƙungiyar agaji ta Oxfam, hukumomin bayar da agaji a duniya waɗanda ta ce suna fuskantar ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa, suna fafutukar kai agaji ga 'yan Yemen, duk da matsalar tsaron da suke fuskanta, ga shi kuma sai ƙara ɗaukar sabon salo ne rikicin ƙasar ke yi saboda shugaba Saleh ya ƙi sauka daga mulki kamar yanda ƙasa da ƙasa suka buƙace shi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani