1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matsalar tsaro a Zamfara na kara yin kamari

June 6, 2018

Daruruwan jama'a a kauyukan Wunnaka da Furar Girke a jihar Zamfara na tserewa saboda barkewar tashin hankali da kuma hare haren barayin dabbobi.

https://p.dw.com/p/2z2PN
Nigeria Flüchtlinge
Hoto: Malik Samuel/Ärzte ohne Grenzen

Daruruwa na mutane daga kauyukan Wunnaka da Furar Girke ya zuwa cikin garin Mada da Kwatarkwashi da Gusau da ke jihar Zamfara suna yin kaura domin kaucewa wani sabon tashin hankali bayan kisan wasu mutane biyu da kuma satar dabbobinsu.

Nigeria Boko Haram Anschlag in Maiduguri
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

Wani wanda ya shaida lamarin da kuma bai so a baiyyana sunansa ba ya ce al’ummar yankin na fuskantar matsanancin tashi na hankali na barayin shanu da mutane.

Kafin sabon rikicin na kauyukan Mada, kusan mutane 30 aka kashe a karamar hukumar Anka da ke cikin jihar a wani abun dake nuna ta’azzarar rikicin da ke kara rikidewa da kuma daukar salo da ke da tsoratarwar gaske.

Majiyoyi a jihar sun ce yan ina da kisa sun kai har suna karbar haraji da kisan aure, a wani abin da ke da kusanci da na Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

Nigeria Abuja Babagana Monguno und Abayomi Gabriel Olonisakin
Hoto: picture-alliance/dpa/N. Bothma

Sai dai kuma bayan wani taron manyan hafsoshin tsaro na tarrayar Najeriyar babban sufeton 'yan sandan kasar ya ce suna shirin tura wata rundunar hadin gwiwa ta  jami’an tsaro kusan 2000 da suka kunshi 'yan sanda da sojoji da sauran jami’an tsaro da nufin tunkarar matsalar.

A cewar Sanata Kabiru Marafa da ke wakiltar al’ummar yankunan da ke tsakiyar rikicin yanzu, gazawa ta shugabannin siyasa na da ruwa da tsaki da ta’azzarar rikicin.

Abin jira a gani dai na zaman tasirin sabbin matakan a kokarin kai karshen matsalar wadda sannu a hankali ke neman mayar da yankin sabon fagen rikici mafi girma a kasar