1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Karancin man fetur ya haifar da matsaloli a Najeriya

Uwais Abubakar Idris MAB
February 16, 2022

Birnin Abuja da wasu jihohin Najeriya sun afka cikin matsanacin karancin man fetur duk da alkawarin da mahukunta suka yi na samar da shi. Wannan ya kawo cikas a harkokin yau da kullum saboda ana sayar da shi da tsada.

https://p.dw.com/p/477LJ
Benzin Afrika
Matsalar karancin man fetur ta zama ruwan dare a NajeriyaHoto: picture-alliance/ dpa

Gardama na barkewa a tsakanin dubban masu motoci da babura da ke rige-rigen shiga wani gidan mai a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, saboda mummunan karancin man fetur da ake fuskanta. Wannan matsalar ta durkusar da al'amura a sassa daban-daban na Abuja da ma wasu jihohi da dama na kasar. Sannan ya bude kasuwar bayan fage ta ‘yan bumburutu inda kowace litar man fetur ta kai Naira 700 maimakon Naira 165 a farashin gwamnati.

Muhammad Nasiru wani matashi da na ke sayar da mai a kusa da wani gidan mai a Abujan. Ya ce: ‘'Muna sai da shi a kan Naira 5,500 kowace jarka mai lita goma, man ya yi tsada ne saboda masu babura ne ke shiga gidan mai su shawo shi suna ba mu shi a Naira 3500 zuwa dubu 400 mu kuma mu sayar dubu 5,500''

Nigeria Tankstelle in Lagos
Gurbataccen man da aka shigo da shi daga ketare ne ya haifar da matsalar Hoto: AFP/Getty Images/E. Arewa

Najeriya ta tsunduma cikin wannan matsalar ne bayan samun gurbataccen man fetur da aka shigo da shi a kasar, wanda kwashe shi daga gidajen mai bayan da ya lalata injunan motoci ya zama wahala. Masu ababen hawa na cikin mawuyacin hali dalilin karancin man fetur, inda dogayen layuka suka cike kalilan daga gidajen da ke sayar da man fetur.

Isma'il Musa wani mai abin hauwa da ya shafe lokaci a kan layyin Ya ce "Na fito karfe biyu na daren jiya neman man fetur, ga shi har yanzu karfe 11:30 na safe ban samu ba. Gaskiya ban ji dadi a raina ba. Ni na ma yanke shawarar komawa garinmu ne domin ka bi layi ba ka samu mai ba''

NNPC ta sha alwashin magance karancin man fetur cikin gaggawa

Kamfanin kula da albarkatun man fetur na Najeriyar NNPC ya ba da umurni ga dukkanin "depot" na adana mai da gidajen man NNPC cewa, daga yanzu masu aikin lodin da masu sayar da mai za su yi aiki ba dare ba rana domin shawo kan matsalar.

Benzin Afrika
‘Yan bumburutu na sayar da man fetur da tsada a kasuwannin bayan fageHoto: picture-alliance/ dpa

Daraktan gudanarwa mai kula da harkar Adetunji Adeyemi ya ce suna da wadataccen man fetur a kasar. Ya ce: ‘' Kamfanin NNPC na da fiye da lita bilyan daya na man fetur, amma muna sane da matsalolin da aka samu na rarraba mai a mafi yawan sassan Najeriya saboda matsalar gurbatcen mai da aka samu da ke dauke da sinadarin Methanol wanda muke gyarawa. Fiye da lita bilyan biyu na man fetur zai iso Najeriya daga nan zuwa karshen wata nan domin tabbatar da wadatarsa na fiye da kwanaki 30''

Sai dai ‘yan Najeriya da dama na neman gani a kasa a kan ikirari na wadata kasar da man fetur. Najeriya dai ta dogara ne a kan shigo da man fetur saboda gaza gyara matatun man fetur, kuma ba labarin gina wasu sabbi duk da arzikin da Allah ya hore mata a yanayi na ga koshi ga kwanar 'yunwa.