Matsalar karancin kudi ta haifar da tarzoma a Chadi
September 28, 2016
Da yake tsokaci dangane da dalillan da suka jefa Chadi a cikin wannan yanayi na matsalar tattalin arziki, Farfesa Ahmat Mahamat Hassane malami a jami'ar N'djamena babban birnin kasar, danganta lamarin ya yi da yadda gwamnatin kasar ta kasa yin dogon tsinkaye game da faduwar darajar farashin man fetur da ake fuskanta a duniya wanda kuma shi ne kasar ke tinkaho da shi wajen samar da kudaden shiga:
Ya ce "Gwamnati ba ta yi tsikaye mai kyau dangane da faduwar farashin man fetur a duniya ba, sai kuma ta yi sakaci sosai wajen kula da sauran hanyoyin samar da kudaden shiga ta hanyar haraji da hukumar kwastam wadanda shekaru da dama sune ke daukar nauyin dawainiyar kasar. Kazalika an dinga facaka da kudin kasa, kana an shiga aiwatar da wasu manyan ayyuka na gine-gine ba tare da an dinga la'akari da halin da kasuwar man fetur da kasar ke tinkaho da shi ta shiga ba"
Wata matsalar ta daban da ta taimaka wajen kara jefa kasar ta Chadi a cikin wanann hali na masassarar tattalin arziki ita ce ta yadda Bankin Raya Kasashen Afirka ta Tsakiya ya ki amince wa mahukuntan kasar ta Chadi damar sake taba kudaden ajiyarsu karo na biyu a cikin watanni kalilan.Kuma Farfesa Ahmat Mahamat Hassane na jami'ar N'djamena ya bayyana dalilin da ya sanya bankin ya dauki wannan mataki ga kasar ta Chadi:
Ya ce "Kar ku manta da cewa muna da wani tsari a kungiyar kasashen Afirka ta Tsakiya wadanda ke da banki na raya tattalin arzikin kasashen. Kuma aka yi rashin sa'a man fetur da kasar ta mallaka ba mai yawa ba ne wanda hakan ya sanya sauran kasashe masu arzikin man fetur a kungiyar kamar su Gabon da Kwango da Equatotial Guinea. Kuma ana bada bashi ne gwargwadan darajar kudin yawan man fetur da kasa ta mallaka, da kuma kudaden ajiyarka, alhali mu namu ba su wuce miliyar 50 na Cfa kaidai ba"
Matsalar kudin Chadi ta shaga sukulashif dalibai
Yanzu haka dai gwamnatin kasar ta Chadi ta kai matsayin da biyan albashin ma'aikata dama kudaden alawus na 'yan makaranta da sauran bukatun al'umma na yau da kullum na gagararta. Lamarin da tuni ya soma haifar da guna-guni dama rikidewa zuwa tarzoma a cikin kasar. Sai dai tuni gwamnatin ta dauki wasu sabbin matakai 16 na tinkarar matsalar, matakan da suka hada da rage kudaden da gwamnatin take kashewa musamman kudaden alawus na manyan ma'aikatan gwamnati da shugabannin hukumomin jamhuriya. Sai dai a cewa Farfesa Ahmat Mahamat Hassane na jami'ar N'Djamena da wuya wadannan matakai su yi wani tasiri.
Ya ce "Ni a gani na wannan ba zai isa ba musamman idan jami'an gwamnati za su ci gaba da yin balaguro shi ma shugaban kasa Idriss Deby zai ci gaba da siyasarsa ta kai dauki a wasu kasashe a matsayinsa na shugaban Kungiyar Tarayyara Afirka duk da yake cewa akwai yiwuwar a loakcin taron koli na MDD da ya gudana a birnin New York ba zai rasa neman agaji daga abokanin huldarsa ba"
Abin jira a gani a nan gaba shi ne yadda Shugaba Deby wanda zabensa ya kasance cike da cece-kuce zai iya shawo kan wadannan tagwayen matsaloli na rikicin siyasa da tarzomar al'umma da kuma matsalar tattalin arziki.