1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar cin hanci da rashawa a Afirka

Yusuf BalaDecember 3, 2014

Kungiyar Transparency International ta ce kasashen Somaliya da Sudan da kuma Sudan ta Kudu ke kan gaba wajen cin hanci da rashawa a duniya.

https://p.dw.com/p/1Dyuf
Transparency International Logo

A wannan shekara ta 2014 kasashe 175 ne aka yi nazari a kansu da irin wannan bibiya, da kan zama wata matashiya ga shugabannin kasashe don fadakar da su kan rashin iya tafiyar da mulki da ma wasu kasuwanci da ake a bayan fage da yadda cin hanci da rashawar ke ci gaba da samun gidin zama a wadannan kasashe.

A kididdigar da ta fitar a wannan Laraba Kungiyar ta Transparency International ta nunar da Somaliya da Sudan da kuma Sudan ta Kudu cewa su ke kan gaba. To ko mene ne dalili? Chantal Uwimana ita ce darakta mai kula da sashen Afirka kudu da Sahara a Transparency International a Berlin a nan Jamus.

"Ba wani abun mamaki ba ne idan kasashe irinsu Sudan ta Kudu da Somaliya suka zama na gaba da samun ci gaban tabarbarewar cin hanci da rashawa, saboda sun samu kansu a yanayi na rashin zaman lafiya. Kuwa ko wane irin rashin zaman lafiya, wannan na iya sawa a yi hasashen cewa suna da yawan cin hanci da rashawa."

Matakin tantance kasashe masu fama da cin hanci

Chantal Uwimana Transparency International
Chantal Uwimana ta kungiyar Tranparency InternationalHoto: Transparency International

Hasashe da ka iya sanya shakku, ya sanya tambayar Chantal Uwimana ko wane matakai suke bi dan tantance wadannan kasashe?

"Yadda ake tattara wadannan bayanai abu ne da ke a bayyane, muna tattaro su ne daga kundin bayanai kamar na Bankin Duniya da taron tattalin arziki na duniya da bankin raya kasashen Afirka. Ba wai wani abu ba ne sabo muke da shi ba, muna tattara abin da ke akwai ne sai mu yi nazari mu fitar da wani sakamako mai kunshe da bayanai. Kuma inda bayanan ke fitowa za a ga inda akwai 'yancin albarkacin baki. Misali akwai bayanai kan yadda mutum zai yi kasuwanci a wasu kasashe da dokoki da kasuwancinsu ya kunsa. Ba wai za mu je ba ne muna gudanar da bincike mu zo da sakamako. Da ma akwai bayanan sai dai za mu ce ne kawai ga yadda bayanan suke idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya."

Cin hanci da rashawa na shafar rayuwar jama'a

A dai irin wannan kididdiga da ake dora kasashen kan sikeli daga sifili zuwa dari, duk kasar da ke kasa da hamsin, cin hanci da rashawarta ya ta'azzara da shafar al‘umma ta hanyoyi da dama.

Infografik Korruptionsindex 2014 Englisch
Taswirar kasashen da cin hanci ya fi kamari

To ko wadanne kasashe ne za a ce sun samu ci gaba da yaki da cin hanci da rashawar a nahiyar Afirka? A nan ma Uwimana ta yi karin haske.

"Idan aka kwatanta da shekarar bara, a kasashe irinsu Cote d'Ivoire da Mali an samu ci gaba, ko da yake nazarin da muka yi daga shekarar bara ne zuwa watan Yuni na wannan shekara. An samu ci gaba alal misali a Cote d'Ivoire an samar da dokoki kan yaki da cin hanci da rashawa, wannan ya nuna mai da hankalin kasar kan wannan fafutuka."

Kasashe ma irinsu Najeriya da ke fama da tashe-tashen hankula, na baya-bayan nan ta'addancin Boko Haram, na ci gaba da zama cikin jerin kasashen Afirka da cin hanci da rashawar ya yi musu daurin gwarmai.