Matasan arewacin Najeriya sun yi amai sun lashe
June 9, 2017Kura ta fara lafawa a Najeriya bayan janye batun korar 'yan kabilar Igbo da matasan arewacin kasar suka kudiri aniya domin samun zaman lafiya. Lamarin da ya janyo martani da kungiyoyin masu fafatukar zaman lafiya da kungiyoyin matasan arewa ta tsakiya, a kan bukatar gwamnati ta gaggauta kiran taron kasa da sarakunan Najeriya da malaman addinai.
Duk da gargadin hukumomi da barazana daga jami'an tsaro kan kama kungiyoyin matasan arewa gami da batun cewa za su kori Igbo daga jihohin arewa. Kungiyoyin matasan sun kammala wani taro tattaunawa gami da tafka mahawara na tsawon kwanaki 2, inda kungiyoyin suka sake fitar wata takarda ta janye batun wa'adin da suka bai wa 'yan kabilar Igbo a arewacin kasa, domin kwantar da hankalin jama'a a Nigeria.
Tuni dai shugabannin kungiyoyin da ke fafatukar kawo zaman lafiya suka fara tofa albarkacin bakinsu. Har dattawa daga yankin arewacin kasar suma dai sun gamsu da janye matakin matasan kan wannan lamari.