1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin Yemen na murkushe masu bore

March 1, 2011

Ali Abdallah Saleh ya sauke wasu gwamnonin Yemen biyar daga mukamansu domin ba sa mara masa baya a yunkurin jajircewa a kan karagarr mulki da ya ke yi.

https://p.dw.com/p/10RYO
Ali Abdallah Saleh lokacin wata yizara a Jamus a 2008Hoto: AP

Shugaba Ali Abdallah Saleh na Yemen ya tsige gwamnonin kasar da jihohinsu ke fiskantar zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa. Wani babban na hannu daman shugaban da bai so a bayyana sunansa da kuma ya bayar da wannan sanarwa, ya ce gwamnoni hudu na kudancin kasar da kuma daya a yammacin kasar da wannan mataki ya shafa, ana zarginsu da gaza murkushe boren neman hambarar da shugaba Abdallah saleh a jihohinsu.

Duban 'yan Yemen ne suke ci gaba da zanga-zanga a birane da dama na kasar domin tilasawa shugaban kasa ya sauka daga karagar mulki. Ali Abdallah Saleh da ya shafe shekaru 32 akan karagar mulki, yayi tayin kafa gwamnatin hadaka a wani mataki na neman kwantar da guguwar neman sauyi da ta shafe kusan wata guda ta na kadawa a wannan kasa. sai dai 'yan adawa da sauran masu zanga-zanga sun sa kafa sun yi fatali da wannan tayi nasa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Ahmed Tijjani Lawal