Kasashe sun soki Trump kan Tuddan Golan.
March 22, 2019Kakakin hukumar kungiyar tarayyar Turai da takwaransa na Jamus da kungiyar kasashen Larabawa sun yi Allah wadai da matakin na Trump. Sai dai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi maraba da sanarwar. Wannan sanarwar ta Shugaba Donald Trump kan amincewa da 'yancin Isra'ila na mallakar Tuddan na Golan na zama babbar nasara ta siyasa ga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda shi da sakataren hakokin wajen Amirka Mike Pompeo suka kai wata ziyara a tsohon yankin birnin Kudus ranar Alhamis.
Ya ce: "Shugaba Trump ya kafa tarihi. Da farko ya amince da Birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, ya koma da ofishinn jakadancin Amirka birnin. Ya janye daga yarjejeniya da Iran ya sake kakaba mata takunkumi, yanzu ya yi wani abu muhimmi na tarihi. Ya amince da ikon Isra'ila a kan Tuddan Golan."
A 1967 bayan yakin kwanaki shida a yankin Gabas ta Tsakiya, Isra'ila ta kwace kaso mafi girma na Tuddan Golan din daga kasar Siriya sannan daga baya ta mayar da shi karkashi ikonta, matakin da kasashen duniya ba su aminta da shi ba. Siriya da kawayenta da sauran kasashen duniya a wannan Jumma'a sun yi tir matakin na Trump da suka ce ya saba wa dokar kasa da kasa da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da ma manufar ketare ta Amirka tsawon shekaru 50, da ke daukar Golan a matsayin yankin da ke karkashin mamaya wanda za a tattauna makomarsa tare da Siriya karkashin kwakkwaran shiri na zaman lafiya. Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Siriya ta ce matsayin Amirka dangane da Tuddan Golan da aka mamaye ya nuna karara rashin mutunta dokar kasa da kasa.
A martanin da ya mayar kan batun shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce matakin na Trump ya jefa yankin cikin sabon yanayi na rikici.
"Sanarwar da Shugaba Trump ya dangane da Tuddan Golan ya jefa yankin cikin zaman dar-dar da sabon yanayi na rikici. Ba za mu taba amincewa da matakin halasta mamaye Tuddan Golan ba."
Ita ma gwamnatin Jamus a ta bakin mai magana da yawun gwamnatin Jamus, Ulrike Demmer, ta ce matsayin gwamnatin Jamus bai canja ba kan kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 497 na 1981 da ya yi watsi da matakin Isra'ila na mayar da yankin karkashinta.
"Gwamnatin tarayya na adawa da daukar mataki na gaban kai. Ko da yake bangarori da dama na amfani da yankin suna kai hare-hare kan Isra'ila, amma dole a samar da yarjejeniyar zaman lafiya da za ta kawar da dukkan barazana da Isra'ila ke fuskata daga Tuddan na Golan. Amma a yanzu bai kamata a dagula lamura da zai mayar da hannun agogo baya a kokarin amun masalaha na rikicin yankin ba."
ar kungiyar tarayyar Turai da kungiyar kasashen Larabawa da kasar Rasha da Iran da hukumar mulkin cinn gashin kan Falasdinawa duk sun yi tir da matakin da Shugaba Trump ya dauka suna masu yin kira da a mutunta dokokin kasa da kasa.