1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin karshe na neman tsige shugabar Brazil

Gazali Abdou TasawaMay 11, 2016

A Brazil a wannan Laraba ce 'yan majalisar dattawan kasar ke bayyana matsayinsu kan shirin tsige shugabar kasar Dilma Rousseff daga kan kujerar shugabanci a bisa zargin karbar rashawa

https://p.dw.com/p/1IlST
Brasilien Präsidentin Dilma Rousseff
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Peres

A kasar Brazil a wannan Laraba ce 'yan majalisar dattawan kasar ke bayyana matsayinsu kan shirin tsige shugabar kasar Dilma Rousseff daga kan kujerar shugabanci, lamarin da zai kasance tsani na karshe ga samun hurumin gurfanar da ita a gaban kuliya domin aiwatar da matakin a bisa zargin cin hanci.

Ana dai kyautata zaton 'yan majalisar dattawan za su kada kuri'ar amincewa da matakin gurfanar da shugabar a gaban kotun domin tun kafin kai wa ga zaben, kimanin 50 daga cikin 81 na 'yan majalisar sun bayyana goyon bayansu ga shirin.

A yammacin jiya Talata dai Shugaba Rousseff ta yi wani yinkurin karshe na neman dakatar da wannan shiri ta hanyar shigar da kara a gaban babbar kotun kolin kasar inda ta bukaci da ta dakatar da abin da ta kira juyin mulki.

Idan har 'yan majalisar dattawan suka ba da na'am dinsu ga matakin, to nan take za a dakatar da shugabancin Rousseff har na tsawon kwanaki 180 kafin bayyana sakamakon shari'ar tsigeta daga kan kujerar mulkin a watan Satumba mai zuwa.