1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan rage yawan cunkoso a kurkuku

Ibrahima Yakubu/ MNAOctober 7, 2015

An fara rage yawan hukuncin kisa ko na daurin rai da rai ya zuwa hukuncin daurin shekaru 10 don rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya.

https://p.dw.com/p/1Gk2f
Nigeria - Christlich-muslimischer Dialog Ramadan
Wasu firsinoni da suka ci gajiyar wani shirin afuwa a KadunaHoto: privat

Firsinonin da suka ci gajiyar wannan mataki musamman wadanda suka aikata laifin fashi da makami sun yi nadama kan irin abubuwan da suka aikata da suka sanya aka yanke musu hukunci daurin rai da rai. Lamarin dai ya sanya su kwashe shekaru da dama a kurkukun cikin mummunan yanayi.

Ire-iren wadannan gidajen kurkuku dai a Najeriya suna cike ne da masu miyagun laifuffuka daban-daban inda ake hada su da masu aikata kananan laifi a wuri daya kuma yawan mazauna kurkukun a kullum karuwa yake. To sai dai akwai wurare na daban da ake kebe wa masu daurin rai da rai.

Yanzu haka don tabbatar da rage cunkoso a wadannan kurkukun, wasu gwamnoni sun yi afuwa ga tsaffin mazauna gidajen yari da aka yanke masu hukuncin kisa ko na rai da rai shekaru 10, saboda irin shekarun da suka dauka don canza masu rayuwa.

Gwamnatin jiha na da hurumin yi wa firsina afuwa

Abubakar Garba daya ne daga cikin jami'an kula da gidajen yarin Najeriya a Kaduna wanda ya yi karin haske:

"Dokar kasa ta bai wa Gwamna damar yin afuwa ga jama'ar jaharsa. Yin haka babu shakka zai rage matsalolin cunkoso da wasu matsalolin da ke addabar kurkukun jihar Kaduna saboda yawan jama'a. Wannan gidan yarin na da shekaru sama da 100. An gina shi ne domin jama'ar Kaduna, to amma yawan al'umman da ke cikinsa ya wuce yadda aka tsara shi."


Nigeria Folteropfer Archiv 2013
Gana wa firsinoni azaba ba bakon abu ba ne a NajeriyaHoto: Amnesty International

Domin canja fasalin rayuwar mazauna kurkukun Kaduna, masu kananan laifin da suka kammala karatun firamare za su ci-gaba da karatunsu na sakandare a cikin gidajen yarin. Ana kuma shirye-shiryen bullo da tsarin yadda za su fara karatun jami'a yayin da suke a kurkuku inji Controller Abubakar Garba.

"Muna da wuraren daukar darussa, kuma yanzu haka Kwamishinan alkalai na shirye-shiryen gana wa da Kwamishinan ilimi kan yadda za a bullo da hanyoyin tallafa wa mazauna wadannan wurare don gyara masu rayuwa."

Har kullun dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam suna ci-gaba da yaki don ganin an haram hukuncin kisa ko yanke tsattsauran hukunci ga masu laifuffuka a fadin kasar.