Mataimakiyar shugaban Amirka ta fara ziyara a Ghana
March 27, 2023Mataimakiyar shugaban Amirka Kamala Harris ta isa kasar Ghana a wannan Lahadi a matakin farko na ziyarar da ta fara a wasu kasashen Afirka domin karfafa huldar diplomasiya tsakanin Amurka da nahiyar.
Kalaman farko da mataimakiyar shugaban ta furta bayan saukarta a birnin Accra ta ce ''Ta dade tana cikin zumundin jiran wannan rana wacce za ta buda sabon babin hulda a tsakanin Amurka da nahiyar Afirka da dama suke da alaka mai cike da tarihi.''
Daga cikin batutuwan da Harris za ta tattauna da Shugaba Nana Akufo Ado ana sa ran za ta tabo batun barazanar sauyin yanayi da yaki da karancin abinci da kuma batun kara saka hannayen jari a Nahiyar ta Afirka.
Kamala Harris mataimakiyar shugaban kasar ta Amirka za ta share kwanaki uku a Ghana inda za ta gana da kungiyoyin dalibai da na 'yan kasuwa da kuma kungiyoyin fararen hula na kasar kafin ta daga a ranar Laraba da ke tafe domin zuwa kasashen Tanzaniya da kuma Zambiya.