1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Mataimakiyar firaministar Kanada ta ajiye aiki

Suleiman Babayo AMA
December 17, 2024

A kasar Kana an shiga rudanin siyasa bayan mataimakiyar firaministar kasar Chrystia Freeland ta ajiye aiki, abin da ake dangantawa da rikici tsakanin mambobi jam'iyya mai mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/4oHEO
Kanada | Chrystia Freeland
Chrystia Freeland mataimakiyar firaministar Kanada da ta ajiye aikiHoto: Spencer Colby/The Canadian Press/empics/picture alliance

Mataimakiyar Firaministar Kanada kana ministar kudi, Chrystia Freeland ta yi murabus daga bakin aiki kuma tana cikin manyan ministocin gwamnatin Firaminista Justin Trudeau. Wannan matakin ya janyo tambayoyi game da matsayin firaministan.

Karin Bayani: Justin Trudeau zai yi wa'adi na uku

Tuni masu adawa na bangaren masu ra'ayin mazan jiya suka nuna irin radanin da gwamnatin kasar ta Kanada ta shiga, na samun sabani tsakanin mambobin jam'iyya mai mulki.