SiyasaTurai
An ci tarar mata saboda tauye hakkin mazan Faransa
December 16, 2020Talla
Ofishin magajin garin Paris da ya yi wannan laifi tun a shekara ta 2018, ya nada mata guda 11 a manyan mukamai sannan ya nada maza guda hudu, abin da ke nufin an yi wa maza danniya ke nan.
Wannan kuma ya saba wa dokar daidaiton jinsi da aka kafa a Faransa a shekara ta 2013 wace ta yi tanadin cewa daga lokacin kada a sake nada wani jinsi ya haura kaso 60 cikin 100 na manyan mukaman gwamnati. Sai dai da ta ke mayar da martani game da tarar Euro 90,000 da aka ci su, shugabar ofishin magajin garin Paris Anne Hidalgo ta ce matakin ya saba ka'ida kuma abu ne mai matukar hadari.