1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata na koyon sanao'in hannu a Bauchi

Aliyu Muhammad Waziri
January 23, 2018

Rashin ayyukan yi a tsakanin matasa musamman mata, ya sa wani matashi bude cibiyar koyar da sanao'in hannu domin rage radadin babu da ake fama da shi a Najeriya.

https://p.dw.com/p/2rMff
ScreenshotsDW Sendung eco@africa
Hoto: DW

Sadik Abdullahi Benzima matashi ne mai kishin al'ummar jihar sa ta Bauchi, ya bayyanawaa DW Hausa abin da ya ja hankalin sa bude wannan cibiya." Na duba na gani cewar rayuwar da ake ciki a yanzu akwai bukatar taimako, in ba haka ba ba bu yadda za a tsira."

Matashin ya ce ya fara bude cibiyar koyon sana'ar ne da mata 2,000 wadan da ake tallafamusu ta fannonin daban-daban, musamman dinkin hula, yin sabulu koyar da girki da saka da dai sauransu.

Sadik ya ce a yanzu haka cibiyar na da dalibai akalla 8,000 kuma babu mai biyan ko sisin kobo kamin a shiga, dalibai da ke samun horo sun yaba da yadda kwalliya ke biyan kudin sabulu daga irin yunkurin matashin ganin yadda suke iya sarrafa abubuwa da hannunsu kuma a sayar da su a wajen jihar.

Sai dai Sadik Abdullahi Benzima ya ce yana fuskantar barazana daga hukumar kula da mata da matasan jihar Bauchi bisa wani yunkuri na kwace cibiyar.