Mata masu taka rawa a kwallon kafa
Kasashen Ostireliya da New Zealand za su dauki nauyin gasar kwallon kafa ta mata ta duniya karo na tara. Fitacciyar 'yar wasan Amurka Alex Morgan ka iya kare kambunta karo na biyu a jere, amma akwai wasu 'yan wasan.
Alexandra Popp: Jamus
A gasar cin kofin kwallon kafa na zakarun nahiyar Turai a 2021 da aka yi a Ingila, "Poppi" ta jagoranci Jamus har zuwa wasan karshe da mai masaukin baki Ingila. Hakan ya janyo farin ciki ga kungiyar ta Jamus. A gasar da Ostireliya da New Zealand za su dauka, 'yar wasan gaba ta kungiyar VfL Wolfsburg za ta jagoranci 'yan wasan Jamus a matsayin kyaftin.
Alexia Putellas: Spaniya
'Yar wasan Barcelonan ta lashe gasar zakarun Turai ta 2023, inda ta lallasa Alex Popp da VfL Wolfsburg. A 2021 da 22, ta samu kyautar 'yaar wasa mafi kwkarewa ta shekara ta FIFA Ballon d'Or da kuma ta UEFA. Ta lashe gasar La liga sau shida da kuma kofin zakarun Turai sau biyu. Sai dai har yanzu ba ta lashe gasa cin kofin duniya da kungiyarta ta kasa a Spaniyan ba.
Asisat Oshoala: Najeriya
Daya daga cikin zakakuran 'yan wasan kwallon kafa na Afirka, Oshoala ta zama 'yar wasan Afirka ta farko da ta lashe gasar zakarun Turai da Barcelona. A 2014, ta lashe gurbi na biyu a gasar kwallon kafar mata 'yan kasa da shekaru 20, ta zama 'yar wasan Afirka mafi kwarewa a shekarar da ma 2016 da 17 da 19 da 2022. An fitar da Najeriya a zagayen rukuni, a gasar duniya ta farko da ta halarta a 2015.
Marta: Brazil
Da shekaru 37 "'yar wasan da ba ta tsufa" Marta za ta halarci gasar karo na shida, tare da fatan samun damar daukar kofin. Marta ta kusa daukar kofin yayin da ta halarci gasar ta duniya karo na biyu a 2007, sai dai Jamus ta hana Brazil samun damar. Daga baya Brazil an yi waje da Brazil din a wasan dab da na kusa da na karshe wato quarterfinals a 2011 kana a zagayen 'yan 16 a 2015 da 2019.
Alex Morgan: Amurka
'Yar wasan da ke rike da kambu Morgan na kan ganiyarta, inda tauraruwarta ke haskkawa. A gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka fafata a Faransa 2019, Morgan ta kasance guda cikin 'yan wasa shida da suka kai wasan karshe har sau uku yayin da Amurkan ke kokarin kare kambun da ta lashe a 2015. Sai dai zai yi wuya ta sake kare kambun, saboda kasashe da yawa na nema.
Barbra Banda: Zambiya
Yayin da suke tunkarar gasar ta duniya, fatan 'yan Zambiya na kan 'yar wasan gaba Barbra Banda. Ta shiga kanun labarai, bayan da zama 'yar wasa mace ta farko da ta zura kwallaye uku a raga a wasa daya yayin gasar Tokyo Olympics. Kana ta sake mamaye kanun labaran, sakamakon hana ta buga wasan cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka saboda gwajin kwayoyin halitta ya nuna tana da na maza mai yawa.
Pernille Harder: Denmark
Ana yi mata kallon daya daga cikin kwararrun 'yan wasa mata a duniya, Harder ta kasance 'yar wasa mafi tsada har zuwa 2022. 'Yar wasan gaban da ta koma Bayern daga Chelsea, ba ta cikin 'yan wasa masu farin jini a Denmark. Ko 'yar wasan mai shekaru 30, za ta haura wasannin uku a matakin rukuni kan wasannita na kasa da kasa 140 da ta halarta da kuma matsayi na biyu a gasar EURO 2017.
Ada Hegerberg: Norway
Mai shekaru 27 na wasa da kungiyar Olympique Lyon tun 2014, tare da taimaka musu wajen samun nasarar taka rawar gani a gasar kofin kalubale ta mata ta lashe kambu shida daga 2016 zuwa 2020 da kuma 2022. Sau guda 'yar wasan farko da ta lashe kyautar mafi kwarewa ta FIFA Ballon d'Or a 2018 ta kai wasan karshe na cin kofin zakarun Turai, inda Jamus ta lallasa ta da ci daya mai ban haushi a 2013.
Mary Fowler: Ostireliya
Mai shekaru 20 'yar wasan gaba ta Manchester City, za ta zama 'yar wasa mafi soyuwa a kasarta. Wasan da za ta yi a gida, zai szama gasar kwallon kafa ta duniya ta biyu da Fowler ta halarta duk da karancin shekarunta. Ta bayyana a "Matildas" a 2018, Fowler ce 'yar wasa mafi karancin shekaru a gasar 2019 da aka fafata a Faransa. Norway ta kore su a zagayen 'yan 16, amma suna fatan nasara a bana.
Keira Walsh: Ingila
A 2022, Walsh ta maye gurbin Pernille Harder a matsayin 'yar wasa mafi tsada. Ta koma Barcelona da ga Manchester City a kan farashin kusan Euro dubu €500 tare da lashe kambunta na farko a gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Turai da Ingilan bayan lallasa Jamus da ci biyu da daya. An zabi Walsh 'yar wasa mafi kwarewa a wasan. Ana kaunarta da 'yan wasan Ingilan, a kwallon kafar duniyar.
Saki Kumagai: Japan
Mai shekaru 32, 'yar wasan baya ta Bayern Munich din za ta kasance kyaftin din Japan yayin da suke kokarin lashe gasar. A 2018 Kumagai ta fara bugawa kasarta, kuma tana cikin 'yan wasan da suka lashe gasar a Jamus a 2011 da lokacin da suka gaza kare kambunsu. Bayan halartar gasar sau biyu a jere, Netherlands ta yi waje da Japan a zagayen 'yan 16 a 2019.