1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu zanga zanga sun sake bazama titunan birnin Moscow

December 24, 2011

Dubban jama'a sun sake kwarara titunan birnin Moscow domin adawa da maguɗin da suka ce an tafka a zaɓen majalisun dokokin da ya gabata, lamarin dake zama ƙalubale ga Valdimir Putin.

https://p.dw.com/p/13YrV
Demonstrators hold Russian opposition flags during a rally protesting against election fraud in Moscow, Saturday, Dec. 24, 2011. Tens of thousands of demonstrators rallied in the Russian capital Saturday in the largest protest so far against election fraud, signaling growing outrage over Prime Minister Vladimir Putin's 12-year rule. (Foto:Alexander Zemlianichenko/AP/dapd)
Masu zanga zangar adawa a RashaHoto: dapd

A wani mataki na nuna ƙosawa da shekaru goma sha biyu na mulkin Firaminita Valdmir Putin dubban jama'a a Rasha sun sake fita zanga zangar adawa akan tituna suna masu jinjinawa 'yan adawa tare kuma da yin shaguɓe ga fadar gwamnatin ta Kremlin. Zanga zangar ta Moscow ta fi makamanciyarta da ta gudana makonni biyu da suka wuce, abin da ake dangantawa da cewa ita ce zanga zanga mafi girma ta nuna rashin amincewa da gwamnati tun bayan faɗuwar tarayyar Soviet a shekarar 1991. Zanga zangar baya bayan nan a Moscow da sauran biranen Rasha sun dakushe martabar Putin wanda ke shirin sake ɗarewa shugaban ƙasar a zaɓe mai zuwa a watan Maris. Mahukunta a fadar Kremlin ɗin dai sun yi alƙawarin gudanar da sauyi da zai bada damar shigar jam'iyyu da dama domin yin gogayya a zaɓɓuka na gaba. Sai dai kuma masu zanga zangar sun ce za su cigaba da aniyar su ta ganin an sake gudanar da zaɓen majalisun dokokin da aka yi a ranar 4 ga watan Disambar da ya gabata wanda suka ce yana cike da maguɗi.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi