Masu zanga-zanga 13 sun mutu a Najeriya
August 2, 2024A cikin sakon da kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta wallafa a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya, ta ce an kashe mutum shida a garin Suleja da ke kusa da birnin tarayyar kasar, Abuja yayin da mutum hudu suka rigamu gidan gaskiya a garin Maidugri da ke arewa maso gabashin kasar, wasu mutum uku suka gamu da ajalinsu a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.
Karin bayani: Zanga-zanga na neman zama rudani a Najeriya
Kungiyar ta zargi jami'an 'yansanda da kisan masu zanga-zangar lumanar. Sai dai rundunar 'yansandan Najeriya ta musanta zargin da ake yiwa jami'anta. Babban Sifeta Janar na 'yansandan kasar, Kayode Egbetokun ya ce sun yi shirin ko-ta-kwana domin dakile duk wata bazarana ga zaman lafiya. Wasu rahotanni sun kuma yi nuni da cewa, 'yansanda sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu boren da suka fito a rana ta biyu.