Bundesliga: 'Yan kallo na murnar dawowa
May 15, 2020Tuni dai kafafen yada labara kamar Freedom Radio da sauran tashoshi a kasar, sun kammala shiryawa tsaf domin yada shrhin gasar ta Bundesliga kai tsaye. Momammed Mohamed da ke gabatar da sharhin Bundeligar a tashar ta Freedom, ya bayyana cewa ya fara wani gangami ga matasa akan faidar sanya takumkumi domin yakar cutar coronavirus. Ita kungiyar Bundesliga Fans club da ke Kaduna karkashin jagorancin Malam Abiola mai Bayern Munich ta nuna farin cikinta, inda ma ya bayyana irin tsare-tsare da suka gudanar a gidajen da ake haska wasannin kwallon kafar kai tsaye. Ya kara da cewa suna fadakar da masu sha'awar kallon wasannin kan muhimmancin bayar da tazara da kuma sanya takunkumi.
Dokokin na da muhimmanci
Abiola ya kara da cewa sun amince da dukkanin dokokin da aka shimfida tsakanin 'yan wasa, kuma a ganinsu wannan wata hanya ce ta daukar matakan rage yaduwar cutar tsakanin 'yan wasan da ma 'yan kallo. Ga alamu dai, dokar takaita zirga-zirga da gwamnatin jihar Kaduna ta sanya, za ta takura masu haska wadannan wasanni.
Kwamared Mohammed Shu'aibu dai, na da wani gidan kallon wasan kwallon kafa a Kaduna da ke nuna wasannin Bundesliga kai tsaye: Muna maraba da matakin komowa wasannin Bundesliga a wannan lokaci, kasancewa Jamus ita ce kasa ta farko a cikin dukkanin kasashen duniya da ake gudanar da wasannin lig-lig na kwallon kafa, da ta fara komawa fagen wasa a irin wannan lokaci. Babbar matsalar da muke fuskanta a wannan lokacin ita ce dokar da hukumomi suka saka ta hana taruwar jama'a, ba za mu taba taka dokar kasa ba, a saboda haka babu tabbacin cewa za a bude gidajen haska wasannin, domin gudun kada hukumomi su dauki matakan rufe ire-iren wadannan wuraren da ke tara matasa masu zuwa daga wasu wuraren domin kallon wasannin na Bundesliga.
Sani Donga da ke kallon Bundesligar a gidajensu, cewa ya yi su kam jira kawai suke yi a koma taka-ledar. Masu sharhi kan harkar wasanin motsa jiki a Najeriya dai, sun nunar da cewa dawowar wasannin Bundesligar wani abun alfahari ne ga kungiyoyin masoya wasannin kwallon kafar a Najeriya. Mr Diji Obadiah Haruna shi ne mataimakin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya "Super Eagles," ya ce sun ji dadin dawowar gasar Bundesligar ta kasar Jamus, kuma suna bukatar ganin dukkanin sauran wasanin kasashen nahiyar Turai sun dawo wajan fafatawa. A cewarsa matasa sun gaji da zama a gida.