Masu sa ido sun isa kasar Yemen
December 22, 2018Talla
Tawagar wacce ta samu jagoranci na Patrick Cammaert janar din soja mai ritaya daga kasar Holand ta fara sauka a birnin Aden inda halastacciyar gwamnatin da al'ummomin kasa da kasa suka amince da ita take.
A cewar jami'an gwamnatin kasar ta Yemen a birnin Aden Cammaert zai gana da shugabanni kafin daga bisani ya kama hanya zuwa birnin Sanaa babban birnin kasar inda 'yan tawaye suke kana daga bisani ya kama hanya zuwa birnin Hodeida.
Wannan dai na zuwa kwana guda bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura jami'ai masu sanya idanu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a kasar Sweden a kokarin samun zaman lafiya a kasar ta Yemen.