1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu bukata ta musamman na cikin dimuwa

Abdoulaye Mamane Amadou
December 3, 2020

Human Rights Watch ta ce rayuwar masu bukata ta musamman a zirin Gaza na cikin tsanani a sakamakon toshe hanyoyi da Isra'ila ta yi baya ga rashin shugabanci nagari daga Hamas mai iko da Gaza.

https://p.dw.com/p/3mB8K
Gaza Streifen | Rauchwolke nach Luftangriff der Israelis
Hoto: Reuters/M. Shana

A wani kiyasin da hukumar ta yi ya nuna cewa mutum miliyan biyu ne ke cikin tsaka mai wuya tun bayan da mahukuntan Isra'ilan suka dauki matakin toshe hanyoyin a shekarar 2007. Kungiyar ta ce akwai bukatar magance matsalar domin inganta rayuwar wadannan mutanen.

Ranar uku ga watan Disambar kowacce shekara ce Majalisar Dinkin Duniya ta kebe don tunawa da masu bukata ta musamman a duk fadin duniya.