Masar: Magance rikicin Gabas ta Tsakiya
May 17, 2021A wata ganawar da ya yi da 'yan jarida a yayin da yake halartar wani taro a birnin Paris na kasar Faransa, shugaban kasar ta MasarAbdel Fattah el-Sisi na ya fadi irin kokarin da kasarsa ke yi, na dakatar da zub da jini tsakanin bangarorin biyu: "Muna aiki tukuru, domin kawo karshen wannan dauki ba dadin na take da kuma ma nan gaba. Dola ne a magance abin da ke janyo wannan rikicin da a ko yaushe yake jawo tashin hankali a wannan yankinmu."
Karin Bayani: Fargaba kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa
Ita ma kasar Saudiyya wacca a karon farko cikin shekarun baya-bayan nan take kakkausar suka ga Isra'ilan, a yayin taron kungiyar kasashen Musulmin Duniya da aka shirya a Riyadh, ministan harkokin wajenta Yarima Faisal Farhan ya nuna goyan bayan Masara yunkurin da take na kawo karshen rikicin da gaggawa: "Domin bayyana damuwa ga irin cin zarafin da Isra'ila ke yi wa al'ummar Falasdinawa da keta hurumin Masallacin Al-Aqsa mai alfarma da birnin Kudus, bayan da ta sa kafa ta shure dukkanin kudadare-kudaren kasashen duniya, mun yi tir ga wannan aikin cin zalin da kuma goyan bayan duk wani yunkurin takawa Isra'ila birki, ciki har da kokarin da kasashen Masar da Jordan ke yi."
Shugaban Amirka Joe Biden wanda ya ce yana goyan bayan Isra'aila na matakan kare kanta da take dauka, shi ma ya ce yana ta kokarin ganin an tsagaita wuta: "Falalsdinawa da 'yan Isra'ila sun cancanci zaman lafiya da kwanciyar hankali, cikin yanayin 'yanci da walwala da bunkasar tattalin arziki gami da cin moriyar tafarkin dimukuradiyya. Gwamnatina na ci gaba da tuntubar bangarorin biyu da masu ruwa da tsaki, domin samar da dauwamammen zaman lafiya a yankin."
Karin Bayani: Tashin hankalin Israila da Falasdinawa a Kudus
Ga dukkan alamu dai wannan yunkurin da ake ta yi, ba zai sanya Isra'ila ta shiga taitayinta ba, yadda aka jiyo firaministan na Isra'ila Benjamin Netenyahu nasa kafa yana fatali da wannan yunkurin yayyafawa ricikin wuta: "Isra'ila na yin duk abun da ya wajaba domin kare 'yan kasarta da fararen hular Falasdinawa. Babu batun ragawa 'yan ta'adda na Hamas da Jihadil Islami, wadanda ke da alhakin jefa Falasdinawa da al'ummar Isra'ila cikin halin kaka-ni-ka-yi. Za mu gasa wa shugabanninsu aya a hannu. Ina kara godiya ga kawayenmu a kasashen Turai da suke goyan bayanmu, musammama shugaban Amirka Joe Biden kan irin goyan bayan da yake bai wa kasata wanda ba ya misaltuwa."
Kungiyar Hamas a ta bakin wani jigonta, Isma'il Haniya ta ce a shirye take da harbawa Isra'ila rokoki na tsawan watanni shida: "Masu fafutuka ba mu da wata bukata banda janyewar Isra'ila daga Masallacin Al-aqsa da Kudus da ma ba mu damar kafa kasarmu ta Falalsdinawa. A shirye muke da ci gaba da yakin sai baba ta gani, domin cimma wannan burin da izinin Allah."
Masharhanta dai na daukar hare-haren Isra'ila kan gine-gine da fararen hula da suka sabawa dokokin yaki, a matsayin gazawa musamman ma bayan da babban hafsan sojojin kasar ya sanar da soke batun tura dakarunsu domin kai samame ta kasa.