Masar za ta ci gaba da yaƙar 'yan ta'adda
October 25, 2014Talla
Shugaban ƙasar Abdel-Fattah al-Sissi ne ya bayyana hakan inda ya ke cewar wasu ne daga waje ne ke fafutukar ganin sun karya kashin bayan Masar, to sai dai bai yi ƙarin haske game da wanda ya ke zargi da kai harin ba. Al-Sisi ya kuma ce gwamnatinsa za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta daƙile dukkannin wani yunƙuri na 'yan ta'adda a duka sassan kasar ko da dai a cewarsa hakan zai ɗau tsawon lokaci amma ya ce ba za su gajiya ba sai sun kai ga ci.
Gwamnatin Masar ɗin dai ta sanya dokar-ta-ɓaci a yankin na Sinai sannan ta ware kwanaki uku domin yin zaman makoki na waɗanda suka rasu sakamakon harin da aka kai.