1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar na muradin shiga kungiyar BRICS

March 26, 2013

BRICS da ke wakiltar al'umma sama da biliyan uku dai, ta na zama wani bangare da hankalin Duniya ya koma kai a maimakon Amurka da Turai da a baya suka fi tasiri.

https://p.dw.com/p/184NL
South Africa's President Jacob Zuma (R) welcomes China's President Xi Jinping for a working visit to South Africa, in Pretoria March 26, 2013. REUTERS/Siphiwe Sibeko (SOUTH AFRICA - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Gamayyar kasashen Brazil, Rasha, Indiya, China da Afrika ta kudu da aka fi sani da suna BRICS, ta kasancewa kungiyar kasashe da tattalin arzikinsu ke ci gaba bunkasa. Kungiyar dake wakiltar al'umma sama da biliyan uku dai, ta na zama wani bangare da hankalin duniya ta koma kai a maimakon Amurka da turai da a baya suka fi tasiri. A taronsu na farko a Afrika ta kudu, kungiyar na neman wasu hanyoyi na kara karfafa tasirinta a Duniya.

A takaice dai ana kiran wannan kungiya BRICS amma sunanta na Iya sauyawa zuwa E-BRICS, kasancewa a wannan taron dake gudana a birnin Durban din Afrika ta kudu, shugaban kasar Masar Mohammed Mursi na muradin ganin cewar kasarsa ta samu hadewa a wannan kungiya ta masu fada a ji, wadda ke wakiltar kashi 40 daga cikin 100 na al'ummar duniya.

Sai dai sakamakon binciken gidauniyar Bertelsmann dake nan Jamusna nuni da cewar, akwai muhimman batutuwa biyu daya kamata kungiyar ta BRICS tayi nazari a akansu, gyare gyaren tsarin siyasa da batun rashin adalci tsakanin al'umma. Kamar yadda mai bincike a gidauniyar Najim Azahaf ya nunar.

Logo BRICS-Gipfel 2013 in Durban / Südafrika

Ya ce " binciken kowanne daga cikin kasashen dake cikin kungiyar na nuni da cewar, ana fama da matsalar rashin adalci a tsakanin al'umma. Ina ganin idan kasashen zasu dauki matakai na farko na shawa kan wannan matsala, wanda ke da muhimmanci wajen bunkasar tattalin arzikinsu dama rayuwa, babu shakkakasashen kungiyar ta BRICS zasu dada samun ci gaba".

A cewar Najim Azahaf dai taron na wannan shekara a Afrika ta kudu dake zama kasar karshe da ta hade a kungiyar ya dace, duk da cewar kasar na fuskantar matsaloli da suka danganci rayuwar al'umma..

Ya ce " yana da matukar muhimmanci ayi taka tsantsan wajen danganta matsalolin kasashen dake cikin wannan kungiyar da junasu, amma dai a fili take cewar kasar Afrika ta kudu na fama da matsanancin matsalar rashin adalci tsakanin al'ummarta".

Kungiyar ta BRICS dai na muradin kafa bankin raya ci gaba mai karfi, wadda zata iya zama tankar babban bankin Duniya ko kuma hukumar bada lamuni ta Majalisar Dunkin Duniya, wadanda a yanzu sune manyana msana'antu na kudi a duniya, kuma tuni magabatan wannan kungiya suka amince da kafuwar a taron nasu dake gudana a birnin Durban din Afrika ta kudu. Kazalika batun samar daasusun ajiya na hadakar kasashen. Tuni dai bankin duniya ta amince da kafuwar bankin, bisa gargadi. A yanzu haka dai ana nazarin inda za'a kafa bankin tsakanin biranen Cape Town, Mosko da Shanghai..

REFILE - CORRECTING TYPO IN "PEOPLE'S" Brazilian Minister of Finance Guido Mantega (L) and Chinese Minister of Finance Lou Jiwei smile after signing a memorandum of understanding between the Ministry of Finance of the Republic of Brazil and Ministry of Finance of the People's Republic of China on Bilateral Cooperation in Macroeconomic, Fiscal and Financial Policies at the 5th BRICS Summit in Durban, March 26, 2013. REUTERS/Rogan Ward (SOUTH AFRICA - Tags: BUSINESS POLITICS)
Ministocin kudi na Brazil da China-Guido Mantega, Lou JiweiHoto: Reuters

Taron nab birnin Durban na samun halartan sabon shugaban kasar China Xi Jinping, wanda ke ziyararsa ta farko a wata kasar ketare tun bayan samun wannan mukami, mutuminda kuma hankali ya koma kansa a cewar Peter Draper kwararre kan kungiyar ta BRICS a makarantar nazarin harkokin cinikayyar dake birnin Johanesburg.

Ya ce " a kasuwance BRICs na nufin, kasar China da sauran. Dangane da haka ne ziyarar farko da shugaba Xi Jinping keyi a wannan taro yana da matukar muhimmanci. Hakan na nuni da cewar China na la'akari da mihimmancin kungiyar ta BRICS. Suna wa BRICS kallon kungiyace wadda tamkar daidai take da kungiyar kasashe masu ci gaban masana'antu ta G7".

Manazarta sun shaidar da cewar taron zai yi nazarin irin sauyi da aka samu dama kuma harkokin siyasa musamman nasu da rikicin yankin gabas ta tsakiya da halin da ake ciki dangane da Iran, Siriya dama Afganistan, inda ake saran matsayinsu zai kasance daya.

A hukumance dai har yanzu babu wani martani dangane da yunkurin kasar Masar na neman hadewa a kungiyar ta BRICS. Inda a birnin na Durban ake saran shugaba Mohamed Mursi zai sake gabatar da wannan muradi.

( Akwai sauti daga kasa)

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Yahouza Sadissou Madobi