Masanan kimiya sun samu lambar yabo ta Nobel
October 1, 2018Talla
Wannan karramawar da zakakuran masanan suka samu a wannan Litinin na zuwa ne bayan wani gagarumin aiki da suka gudanar a duniyar kimiya inda suka gano dabarun masanan kimiya wajen amfani da garkuwar jikin dan adam wajen yaki da cutar daji ko kansa a Turance. Masanan kimiyar dai sun yi aikin nasu ne a shekarun 1990 wanda ya taimaka wajen samun sauyi da amfani da sabbin dabaru wajen kula da marasa lafiya da suka harbu da cutar daji a hunhu ko a fatarsu.