An bada lambar yabo ta Nobel ta shekarar 2021
October 5, 2021Talla
Masana kimiyyar uku masana kimiyya Klaus Hasselmann dan kasar Jamus da Syukuro Manabe dan asalin kasar Japan, da kuma Giorgio Parisi na Italiya dai sun taka rawa wajen gano bayanai da fahimatar da al'umma wasu muhimman abubuwa na sauyi a duniyar bil'adama ciki har da matsalar sauyin yanayi da duniya ke fuskanta.
Alkalan yanke hukuncin wadanda suka cancanci lambar yabon ta Nobel ta Physics, sun shaidar da cewar masana kimiyyar uku da shekarunsu ya shige 80, tun a shekarun 1960 ne suka dukafa wajen gano tare da fahimtar da jama'a sarkakiya da ke tattre da yanayi wanda zai jagoranci dumamar yanayi, da ke zama tubali ga sauyin da duniya ke ciki a yau.