1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta mayar wa Amirka martani

Mahmud Yaya Azare GAT
October 15, 2019

Shugaban Amirka Donald Trump ya cika alwashin da ya sha na sanya wa Turkiyya takunkumi, muddin ta wuce gona da iri a hare-haren da take kai wa Kurdawa a Siriya. Sai dai tuni Turkiyyar ta mayar da martani kan matakin.

https://p.dw.com/p/3RKJO
Türkei PK Präsident Erdogan
Hoto: Reuters/Murat Kula/Presidential Press Office

A wani matakin da bai zamo na ba-zata ga wadanda suka san halinsa na kwan-gaba kwan-baya ba, shugaban na Amirka wanda da fari, shi da kasar ta Turkiyya ne suka shirya kaddamar da harin kan Arewa maso gabashin Siriyar don samar da tudun-na-tsira ga miliyoyin 'yan gudun hijirar Siriya da ke Turkiyya, amma daga baya ya zare hanunsa daga wannan batun, ya ma janye dakarunsa daga kasar, a wani hannunka-mai-sanda ga Turkiyya da ta yi gaban kanta ta kaddamar da harin. Sai gashi kwanaki uku da fara farmakin na Turkiyya, ya juya mata baya, kamar yadda ya juya wa Kurdawan da Turkiyyar ke yaka baya, yadda a yanzu haka yake goyan bayan shugaban Siriya Bashar al-Asad, wanda ya yi ta siffantawa da shedani masha jinni a baya:


"Idan har Turkiya ta wuce gona da iri a hare-haren da take kaiwa, to za mu yi musu mummunan duka da takunkumin da zai karya tattalin arzikinsu."


Trump din ya kara da nuna goyan bayan duk wata rundunar da za ta taka wa Turkiyya birki kan samamen, ko da kuwa Shugaba Asad na Siriya ne da kawayensa Rasha da Iran. Tuni dai ma,ajin kasar ta Amirka, Steven Mnuchin ya sanar da sanya wa Turkiyyar takunkumin na somun tabi:

USA Trump kündigt Sanktionen gegen Türkei an
Hoto: AFP/S. Loeb


"Mun sanya wa ma,aikatu uku takunkumin da zai fara aiki nan take, kamawa daga ma'aikatar tsaro da  ma'aikatar cikin gida da kuma ta makamashi. Wannan somin tabi ne, idan ba a dakatar da wannan farmakin ba, to za mu dauki matakai mafiya zafi. A shirye muke mu cire wannan takunkumin da zarar Turkiyya ta dauki matakin da ya dace."


Tuni dai shugaban Turkiyyar ya siffanta wannan mataki da cin dunduniyar da ba zai sanya shi dakatar da nausawar da ya ce dakarunsa ke yi dan a tsabtace yankin daga 'yan ta,adda:


"Wannan mataki yana da daure kai. Mutanen da kuka tabbatar da cewa 'yan ta,adda ne, za ku hana mu yakar su. Shin kuna ganin wannan takunkumin naku yana nufin goyan bayan yaki da ta,addanci ne, ko dai kokarin yimar zagon kasa?Ku ba ni amsa."

Türkei/Syrien: Ceylanpinar - Rauch über syrische Stadt Ras al-Ain
Hoto: Reuters/S. Nenov


Tuni dai darajar kudin kasar na Turkiya wanda dama yake ta samun komabaya, ta sake zubewa da digo daya da rabi, tun bayan sanar da wannan takunkumin. Duk da cewa dai, galibin jam'iyyun siyasar kasar ta Turkiya na goyan bayan samamen da dakarunsu ke kaiwa yankin Kurdawan, sai dai ga dukkan alamu murna kan iya komawa ciki idan aka yi la'akari da irin juya bayan da kasashen Yamma suka yi wa Turkiyyar, da kuma yadda dakarun Siriya suka danno don lalata wannan shirin da take zatan zai rage mata matsalar miliyoyin 'yan gudun hijirar da ke kasarta, suke kuma illa ga tattalin arzikinta.))